Discover millions of ebooks, audiobooks, and so much more with a free trial

Only $11.99/month after trial. Cancel anytime.

Mujarrabi
Mujarrabi
Mujarrabi
Ebook68 pages1 hour

Mujarrabi

Rating: 0 out of 5 stars

()

Read preview

About this ebook

A yayin tabbatad da cikan burin nasu, bayan sunyi auren sai Allah ya yalwata dayansu da haihuwar da namiji, dayan kuwa ya jarabce ta da rashin haihuwa.

Hankalinta yayi matukar tashi a game da wannan jarabawar da Allah yayi mata, badon komai ba sai don yadda take da burin samun haihuwar ‘ya mace da kuma yadda take fuskantar barazanar kishiya daga mijinta da kuma surikarta. Mafi yawancin lokaci idan zance ya hadasu, surikar nata take musguna mata da munanan kakalai irin su "guzuma babu haihuwa, saidai aci ayi kashi".

Wannan shine dalilin da yasa ta bazama asibitoci daban-daban, domin gudanar da gwajin mahaifa. Daga karshe dai malaman asibiti sun tabbatar mata da lafiyar mahaifar ta. Don haka sai ta koma gida ta shawarci mijin nata da yaje asibiti shima yayi gwajin domin su gano mai matsalar a tsakanin su. Ashe ita bata sani ba, tun kafin ta fara yawace-yawacen asibitoci ya rigata, kuma yasan da cewar matsalar daga gareshi ne, amma duk da haka ya cigaba da mata kurari da fadar ganganci.

Da ya fahimci cewar yanzu tasan matsayinta kuma zata iya bashi matsala, sai yaci mutuncinta ya wanke zuciyarsa da borin kunya. Sannan kuma ya kara mai-maita mata kalmar “Idan kin ga da dama ki zaga dukkanin asibitocin garin nan su gwadaki ba damuwa na bane, aure ne dai sai na kara.” Ita kuma ta kudurta wa zuciyarta cewar "wallahi bazan taba tsayuwa ina gani ya kawo min kishiya cikin gidan nan ba, don wallahi idan ina ganinta zuciyata zai iya fashewa” Don haka sai tayi shawari da zuciyarta taje ta samo ciki a waje. Ta samu zaman lafiya da surukarta, kuma allah ya cika mata burinta na haihuwar ‘ya mace.

Karanta labarin 'Mujarrabi' domin jin yadda ta kaya. Zaku iya siyan bugaggiyar littafin ta Amazon ko Ebay, sannan kuma zaku iya siya musamman domin karantawa a na'ura mai kwakwalwa (waya ko kwamfuta).

LanguageEnglish
Release dateFeb 1, 2014
ISBN9781311958921
Mujarrabi
Author

Hayat Alsanuzi

Welcome.I'm Al-sanuzi; an avid reader and passionate writer based in Kaduna Nigeria. I'm a seasonal journalist, blogger and social commentator, also the friend of all. My writings are socially and politically motivated. For printed copies of my books check amazon or ebay.

Read more from Hayat Alsanuzi

Related to Mujarrabi

Related ebooks

Mystery For You

View More

Related articles

Reviews for Mujarrabi

Rating: 0 out of 5 stars
0 ratings

0 ratings0 reviews

What did you think?

Tap to rate

Review must be at least 10 words

    Book preview

    Mujarrabi - Hayat Alsanuzi

    Mujarrabi

    Hayat Alsanuzi

    Copyright 2013 Alsanuzi

    Smashwords Edition

    ++++

    License Notes

    Thank you for downloading this ebook. It is licensed for your personal enjoyment only and remains the copyrighted property of the author. This ebook may not be sold, reproduced, copied, or given away, whether for commercial or non–commercial purposes. If you enjoyed this book and would like to share it, please encourage your friends to download their own copy at Smashwords.com, where they can also discover other works by this author. If you're reading this book and did not purchase it, or it was not purchased for your exclusibe use, please go to Smashwords.com and purchase your own copy. Thank you for your support, and for respecting the hard work of this author.

    Please consider writing a review for this book on the retailer's website.

    * * *

    DA FARKO

    Hajiya Basma tayi gaggawan ankara, a yayin da 'yarta Ummi Salma take kokarin hallaka kanta, sulale a tsakiyar dare ba tare da kowa ya sani ba. Dare yayi dare bakajin motsin komai sai kukan gyare da sauran kwari, duhun dare ya mamaye ko ina, baka ganin komai sai dan kankanin hasken da ya haska fuskarta. Ta tsaya cak a bakin rijiya tana sheshshekan kuka.

    Wani zuciyan yana raya mata cewaKi fada kawai ki huta da damuwar duniya' wani zuciyar kuma yana mata gargadi da cewa Ki sani duk wanda ya halaka kansa da kansa, makomarsa jahannama ne. Kuma masifar can daya ta ruba dubun na duniya"

    Tabbas tana fusace, don kwayar idanunta ma kawai ya ishemu kwatance, don sunyi jazur kamar garwashin wuta. Hawaye kuwa zubowa suke tamkar yayyafin ruwan sama. Daga nesa Hajiya Basma ta hangeta a birkice, kanta babu dan kwali kafafunta ko takalma babu. Tana tsaye daf da rijiyar, wanda ko kyakkyawar razana ka mata zata iya afkawa ciki.

    Hajiya ta tsaya daga nesa tace Ummi Lafiyan ki kuwa…? Me aka miki da tsanani haka da har kike kokarin hallaka kanki?

    A razane ta juyo ta dubeta, saboda duk abinda takeyi batayi zaton cewa wani na kallonta ba, cikin kuka tace Wallahi Umma da na tsaya ku daura min aure da Majid gara na kashe kaina Wannan kalma tayi matukar tunzura mahaifiyan nata, wanda har saida yasa ta mance da irin mummunan hatsarin da rayuwan 'yar nata yake ciki tace To indai akan Majid ne, aure kamar an yi shi, kuma wallahi in har ina raye, baki isa ki auri wani bayan shi ba.

    Ba tare da ta tsaya ta sake sauraron wani kalma daga bakin mahaifiyar nata ba, a harzuke ta daka tsalle ‘Wiiii tanjam’ sai cikin rigiya.

    Wayyo Allah na shiga uku, jama'a ku taimake ni Ummi zata mutu a cikin rigiya. Ta waiga gefe da gefe bata ji alamun wani na zuwa ba, gashi babu halin ta bita cikin rigiyar ayi gawa biyu.

    Bata tashi sanin cewa mafarki takeyi ba, saida mijinta ya yanke sallar nafilar da yake, ya rugo cikin dakin a guje yana fadin La, la, Lafiya kuwa? Sai ta bude idanu ta ganta kwance a kan gado, ta wargaza shimfidin, ta shusshure dukkanin matasan dake kan gadon da kafafunta.

    SASHE NA 1

    Guguwar sahara ta taso ta mamaye ko ina, dukkanin mutane da dabbobi suna ta hanzarin neman mafaka kafin ya tsagaita. A dai–dai wannan lokacin ne muka hangi wasu mutane biyu daga nesa sun nufo inda muke. Saboda tsananin yawan kurar dake tashi da ratar dake tsakanin mu da su, bamu ganin komai sai alamun mutane biyu, daya na kan rakumi daya kuma na tafe a kafa rike da ragamar rakumin.

    Bayan sun iso daf da mu, sai muka fahimci cewar ashe Ummi Salma ce a kan rakumin sanye da wando da takalmin 'yan bautar kasa, rigar dake jikinta kuwa yafi karfin a kirashi babban riga, don ya mamaye ta daga sama har kasa, sannan ta sha rawani irin na buzaye, baka ganin komai sai kwayan idanun ta.

    Zagin nata kuwa, wani saurayi ne sanye da kaya irin nata, ya ratayo wasu bakaken jakakkuna irin na ‘yan makaranta. Daya ta gefen hagu, daya kuma ta gefen dama hade da tulun ruwa rataye a kafadar sa.

    Babu shakka duk wanda ya hangesu daga nesa zaiyi zaton cewa bawane tafe da uban gijiyar sa, don ya sa kanshi gaba tafiya kawai yake a tsakiyar sahara baya shayin komai.

    Basu tsaya a ko ina ba sai kofar gidan Ardo Jarma, anan suka yada zango, ya janye ragamar kasa, rakumin ya durkusa a hankali Ummi Salma ta sauko, sannan ya mika mata tulun ruwan dake rataye a kafadarsa, ta bude ta kurba sau uku, tana mai murmushi da nuna alamun jin dadi da farin ciki, har saida ta kore fitinannen kishin dake damunta. Sannan ta mika masa tulun, ta sa hannu ta kunce rawanin dake fuskarta shima ya kunce nasa.

    Tace Inda ace har yanzu ana siyar da bayi, da naje gidan ku na roki mahaifin ka ya siyar mun da kai Sai ya juyo ya kalleta, yayi murmushi

    Yace,

    Enjoying the preview?
    Page 1 of 1