Discover millions of ebooks, audiobooks, and so much more with a free trial

Only $11.99/month after trial. Cancel anytime.

Hajji Da Umrah A Saukake
Hajji Da Umrah A Saukake
Hajji Da Umrah A Saukake
Ebook82 pages32 minutes

Hajji Da Umrah A Saukake

Rating: 0 out of 5 stars

()

Read preview

About this ebook

Da sunan Allah mai rahma mai jinkai. Godiya ta tabbata ga Allah Madaukakin Sarki, muna yabon Sa muna neman taimakon Sa kuma muna neman gafarar Sa, muna neman tsarin Allah daga sharrin kawunan mu da sharrin miyagun ayyukanmu. Duk wanda Allah Ya shiryar da shi babu mai batar da shi, haka duk wanda Ya batar babu mai shiryar dashi. Na shaida babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, Shi kadai bashi da abokin tarayya. Kuma na shaida Annabi Muhammadu bawan Sa ne kuma Manzon Sa ne. Allah shi yi dadin tsira da albarka ga Manzon Sa Annabi Muhammad (SAW) da iyalansa da sahabbansa da duk wanda yabi hanyar su da kyautatawa har ranar tashin kiyama. Bayan haka hajji daya ne daga cikin shika-shikan musulunci guda biyar kuma dukkanin wata bauta a musulunce ba a karbar ta sai anyi ta bisa ilmi kuma bisa koyarwar Manzon Allah (SAW). Manzon Allah yace: “kuzu anni manasika kum” (Ku riki salon aikin hajjin ku daga gareni). “Hajji da Umrah a Saukake” littafi ne dana rubuta shi domin yin bayani game da aikin Hajji da Umrah kamar yadda Manzon Allah ya koyar kuma ya karantar. Na rubuta littafinne da niyyar karantar da alhazai maniyyata aikin hajji, da daliban ilmi da sauran al’ummar musulmi baki daya. Littafin na kasa shi ne bisa babi hudu. Babi na daya zuwa na uku na tattauna ne akan sharudda, rukunai, nau’ukan aikin hajji da yadda ake yin kowane daya daga cikin au’ukan hajjin da abubuwan dake bata hajji. Da kuma muhimman hukunce-hukuncen da suka shafi mata kadai. Sannan babi na hudu kuma na tattauna ne akan ziyara zuwa Madina tare da ladubban ziyarar. Ina rokon Allah madaukakin sarki Ya gafarta wa duk wanda ya karanta wannan littafin, Ya datar dashi sunna da shiriyar manzon Allah (SAW), ya kuma karbe shi gareni a matsayin hidima ga addinin sa. Kuma Allah Ya sakawa wadanda suka taimaka wannan littafi ya tabbata da gidan Aljanna.
LanguageHausa
Release dateAug 22, 2023
ISBN9781312232921
Hajji Da Umrah A Saukake

Related to Hajji Da Umrah A Saukake

Titles in the series (6)

View More

Reviews for Hajji Da Umrah A Saukake

Rating: 0 out of 5 stars
0 ratings

0 ratings0 reviews

What did you think?

Tap to rate

Review must be at least 10 words

    Book preview

    Hajji Da Umrah A Saukake - Dalhatu Zariya Dahiru Muhammadu

    ALL RIGHTS RESERVED

    No part of this publication may be reproduced, stored in a retrieval system, or transmitted in any form or by any means, electronic, mechanical, photocopying, recording, or otherwise, without the prior written permission of the copyright holder.

    Ba’a yarda a sake buga wannan littafi ba, ko wani bangaren littafin ba, ta kowane hanya ba tare da izinin mai littafin ba.

    Hakkin mallaka (m) Dahiru Muhammad Dalhatu

    Email: dahirumuhammaddalhatu@gmail.com

              +2348025684781, +2348097302887

    First Published, August. 2023

    ISBN: 978-1-312-23292-1

    C:\Users\Test\Pictures\ALH. DANJUMA\HAJJ BOOK\978-1-312-23292-1.png

    Publisher:

    logo 1

    Noogul Digital Publishing

    (RC3185897)

    SADAUKARWA

    Na sadaukar da wannan littafin nawa mai suna Aikin Hajji da Umrah a Saukake ga mahaifana, Alhaji Muhammad Dalhatu da Hajiya Juwairiyya Nuhu

    GODIYA

    Godiya da yabo sun tabbata ga Allah madaukakin Sarki. Tsira da amincin Allah su tabbata ga fiyayyen haliyya, manzon Allah (S.A.W).

    Ina mika godiya ta ga Alhaji Dauda Iliyasu tsohon Member JSC Jihar Kaduna da Alhaji Sama’ila Aliyu tsohon kwamishinan kudi na Jihar Kaduna wadanda suka bani shawarar rubuta wannan littafin don muhimmancin sa. Da sauran ‘yan uwa da abokai bisa shawarwarin su har littafin ya tabbata.

    Ina fatan Allah ya hada mu a gidan Aljanna baki daya. Amin

    Dahiru Muhammad Dalhatu

    Zariya.

    ABUBUWAN DAKE CIKI

    ALL RIGHTS RESERVED

    Email: dahirumuhammaddalhatu@gmail.com

    SADAUKARWA

    GODIYA

    GABATARWA

    BABI NA DAYA

    TAFIYA AIKIN HAJJI DA UMRAH

    MATSAYIN HAJJI DA UMRAH

    FALALAR AIKIN HAJJI DA UMRAH

    SHARUDDAN HAJJI

    SHARUDDAN ZAMA MUHARRAMI

    SHIRYE-SHIRYEN TAFIYA AIKIN HAJJI DA UMRAH

    BABI NA BIYU

    RUKUNAN HAJJI DA UMRA

    RUKUNAN HAJJI

    RUKUNAN UMRA

    WAJIBAN AIKIN HAJJJI

    SUNNONIN AIKIN HAJJI

    MAWAQIT

    YADDA AKE DAUKAN HARAMA

    NAU’UKAN HAJJI

    YADDA AKE HAJJIN TAMATTU’I

    YADDA AKE HAJJIN QIRANI

    YADDA AKE HAJJIN IFRADI

    MAHAZURATUL HAJJI (ABUBUWAN DA AKA HARAMTA GA MAI AIKIN HAJJI)

    HUKUCIN WANDA YA AIKATA ABUBUWAN DA AKA HARAMTA GA MAI AIKIN HAJJI

    DAURA AURE:

    RUNGUMAR MACE:

    FARAUTA:

    JIMA’I DA MACE:

    ABUBUWAN DA’AKA AMINCE MAI HARAMA DA AIKIN HAJJI YA AIKATA:

    BABI NA UKU

    GARIN MAKKAH

    DARAJA DA ALFARMAN GARIN MAKKAH

    MASALLACIN HARAMI DAKE MAKKAH.

    YADDA AKE UMRAH

    SA’AYI

    AYYUKAN RANAR TAKWAS GA DHUL-HIJJA (YAUMIT-TARWIYYAH)

    RANAR TARA GA DHUL-HIJJA: (RANAR ARAFAH)

    DARAJAR RANAR ARAFAH

    AYYUKAN RANAR ARAFAH

    MUZDALIFA

    AYYUKAN RANAR GOMA GA DHUL-HIJJA (RANAR BABBAN SALLAH).

    LADUBBAN HADAYA

    AYYUKAN RANAR GOMA SHA DAYA GA DHUL-HIJJA

    AYYUKAN RANAR GOMA SHA BIYU

    AYYUKAN RANAR GOMA SHA UKU GA DHUL-HIJJAH

    TAMBIHI

    DAWAFUL – WADA

    MUHIMMAN HUKUNCE-HUKUNCE DA YA SHAFI MATA KADAI

    WURAREN DA AKE ZIYARA A MADINA:

    KAMMALAWA

    MABINCIKA

    GABATARWA

    Da sunan Allah mai rahma mai jinkai. Godiya ta tabbata ga Allah Madaukakin Sarki, muna yabon Sa muna neman taimakon Sa kuma muna neman gafarar Sa, muna neman tsarin Allah daga sharrin kawunan mu da sharrin miyagun ayyukanmu. Duk wanda Allah Ya shiryar da shi babu mai batar da shi, haka duk wanda Ya batar babu mai shiryar dashi. Na shaida babu abin bautawa da gaskiya sai Allah,

    Enjoying the preview?
    Page 1 of 1