Discover millions of ebooks, audiobooks, and so much more with a free trial

Only $11.99/month after trial. Cancel anytime.

Spiritual Reflections Hausa Translation: English To Hausa Translation
Spiritual Reflections Hausa Translation: English To Hausa Translation
Spiritual Reflections Hausa Translation: English To Hausa Translation
Ebook245 pages1 hour

Spiritual Reflections Hausa Translation: English To Hausa Translation

Rating: 0 out of 5 stars

()

Read preview

About this ebook

”Tunanunnukan Ruhaniya: Littafi Game da Farkawa da Wayewa” littafi ne na wakoki, wanda ya ƙunshi wakoki 200 na Ruhaniya kyauta. Waɗannan waƙoƙin sun haɗa da tunanin da aka gani a cikin litattafai na ruhaniya guda huɗu a cikin “Jerin Litattafai Huɗu Na Farkawa”, ban da wasu da yawa da ba a buga ba tukunna. Babban jigon waɗannan waƙoƙi shi ne Ruhaniya, kowanne yana misalta bangarori daban-daban na “Farkawa” da “Wayewa”.


Tunanunnukan na Ruhaniya: Littafin Farkawa da Wayewa littafi ne na wakoki, wanda ya kunshi kasidu 200 na ruhi kyauta. Waɗannan waƙoƙin sun haɗa da tunanin da aka gani a cikin litattafai na ruhaniya guda huɗu a cikin Jerin Litattafai huɗu na Farkawa, ban da wasu da yawa da ba a buga ba tukuna. Jigon wa]annan waƙoƙi shi ne Ruhaniya, kowanne yana misalta ɓangarori daban-daban na tsarin Farkawa da Wayewa. Ba su da addini, a'a, tunani ne na yau da kullum na ruhaniya game da wayewar ruhaniya. Ruhaniya ita ce imani akwai wani yanki na Ubangiji (Ruhi ko Rai) a cikin kowace rayuwa kuma, saboda wannan, kowace rayuwa tana da Muhimmanci, Daidaito, da Haɗaka. Burina na rubuta duka littattafai guda huɗu a cikin Jerin Litattafai huɗu na Farkawa da kuma wannan littafin waƙa, shine in yi ƙoƙarin farkarwa da taimaka wa wasu, waɗanda suka farka, su ƙara fahimtar menene Wayewa, don haka Tafiya ta Rayuwa za ta iya zama da cikakkiyar fahimta.
LanguageHausa
PublisherTektime
Release dateMay 10, 2022
ISBN9788835444510
Spiritual Reflections Hausa Translation: English To Hausa Translation

Read more from Ken Luball

Related to Spiritual Reflections Hausa Translation

Reviews for Spiritual Reflections Hausa Translation

Rating: 0 out of 5 stars
0 ratings

0 ratings0 reviews

What did you think?

Tap to rate

Review must be at least 10 words

    Book preview

    Spiritual Reflections Hausa Translation - Ken Luball

    littafi mai alaka da jerin litattafai huƊu na farkawa

    Tunanunnukan

    Ruhaniya

    LITTAFI GAME DA FARKAWA DA WAYEWA

    Ken Luball DA Bodhi (JAGORAN RUHI)

    Translator Nuhu Muhammed Ahmed

    Copyright Claimant:  Ken Luball

    Bayanin Marubuci:

    Tunanunnukan Ruhaniya: Littafi Game da Farkawa da Wayewa littafi ne na wakoki, wanda ya ƙunshi wakoki na ruhaniya 200. Waɗannan waƙoƙin sun haɗa da tunanunnuka da aka gani a cikin litattafan ruhaniya guda huɗu a cikin Jerin Litattafai Huɗu na Farkawa, ban da wasu da yawa da ba a buga ba tukun. Jigon waɗannan wakoki shi ne Ruhaniya, kowanne yana misalta fannoni daban-daban na Farkawa da Wayewa. Don fahimtar kowane tunanin da gaske, karanta zuwa 2 ko 3 kawai a rana sannan kayi tunani.

    Ruhaniya ita ce imani akwai wani yanki na Allah (Ruhi ko Rai) a cikin kowace rayuwa kuma, saboda wannan, kowace rayuwa tana da Muhimmanci, Daidaito, da Haɗaka.

    Burina na rubuta litattafai huɗu a cikin Jerin Litattafai Huɗu na Farkawa da kuma wannan littafin waƙa na Ruhaniya, shine in yi ƙoƙari in farkar da taimaka wa wasu, waɗanda suka farka, su fahimci menene Wayewa, don haka Tafiyarsu ta Rayuwa za ta iya kasancewa da cikakkiyar ganewa.

    Bodhi shine Jagorar Ruhi; yana iya yin magana da ni cikin sauƙi yayin da nake rubuta tunaninsa. Ko da yake tafiyata zuwa ga Wayewa ba ta cika ba tukunna, Bodhi, kasancewarsa Jagorar Ruiu, hakika ya waye. Mun rubuta wannan littafi na Tunanunnukan Ruhaniya tare domin duk waɗanda ke neman fara farkawa ko kuma waɗanda suka farka kuma suka nemi ci gaba a kan hanyarsu ta zuwa Wayewa. Su kara koyo game da kowane ɗayan daga cikin littattafai na Ruhaniya a cikin Jerin Litattafai huɗu na Farkawa a yanar gizona:

    http://kenluball.com

    Littattafai huɗu a cikin Jerin Litattafai Huɗu na Farkawa sun haɗa da:

    Yau Zan Mutu: Zabi A Rayuwa

    Jagorar Ruhi: Tafiya Ta Rayuwa

    Natsuwa: Kauyen Fata

    Mafarkin Farin Ciki: Zaɓar Soyeyya akan Tsoro

    Malam Buɗe Littafi

    Ba wasu ba ne wanda dole su canza (Izza).

    Kai ne wanda dole ne ya fara canzawa ta (Ruhi).

    Daga nan ne za ka fara fitowa

    Daga cikin kwakwar ka

    Sannan ka zama malam buɗe littafi.

    Matakai Uku Na Wayeywa

    Matakin Wayewa Na Farko – kasancewarwa cikin Barci

    Matakin farko na wayewa yana farawa ne lokacin da aka haife mu.

    Kamar yadda muke zamantakewa kuma an koya mana abin da za mu yi imani da (Izza),

    Kamar yadda aka bayyan mu ga da kuma yarda da yawancin abubwan al'ummar da aka haife mu a ciki.

    Tare da haihuwarmu, an riga an ƙayyade su waye mu.

    Kalar fatarmu, kasar da aka haife mu, addini,

    Kuma da yawa wasu kwatancen da ɗan adam ya kirkiro sau da yawa suna yanke gobenmu a duniya.

    Mun yi imani waɗannan kwatancen gaskiya ne ta hanyar lura da wasu,

    Karanta game da su a cikin littattafai da jaridu da kallon talabijin da fina-finai.

    Yawancin mutane sun gaskata kuma sun sanya waɗannan bambance-bambancen har ciki, suna ƙara tabbatarwa da kansu

    Sun fi kowa, suna mafi mahimmanci fiye da wani.

    Lalle ne waɗanda suka yarda kuma suka gaskata abin da aka karantar da su, gaskiya ne,

    Duk da Nasarar da suka yi a rayuwa, sun kasance cikin Barci, da

    An kaddara musu yin rayuwa ta tsaka-tsaki,

    Imanin cewa Farin ciki da Ma'anar rayuwarsu zai fito daga Duniya.

    Ba zai fito daga duniya ba.

    Matakin Wayewa Na Biyu– Farkawa

    Wadanda suka farka sukan fara tambaya ko duk abin da muka koya kuma muka yarda da shi

    Ya kasance gaskiya a rayuwa, yayin da muke girma, gaskiya ne.

    Wani ji zai fara bunƙasa a ciki, wanda ba za a iya watsi da shi ba,

    Tambayar ingancin Duk abin da muka taɓa yin Imani da.

    Ko da yake muna iya yin rayuwar nasara, mu kasance masu wadata, shahara,

    Ko wani kwatancen da aka Koyi game da menene nasara,

    Ba ya daina kwantar da rashin jin daɗin da muke fuskanta daga can ciki.

    Damuwar da muke ji tana fitowa ne daga Ruhinmu, wanda yake cikin kowace rayuwa.

    Wasu na iya kiran Ruhi Allah/Rai/Jigo ko kuma su sanya masa wani suna.

    Suna da aka shi da shi ba shine mai muhimmanci ba.

    Yana wakiltar Jagorar mu ta rayuwa kuma yana ba rayuwarmu Ma'ana.

    Mun farka duk lokacin da muka fara jin wani abu ba daidai ba ne,

    Fara tambaya idan abin da muka Koya kuma muka yarda da shi gaskiya ne, mai yiwuwa bai ya kasance ba,

    Farar da mu a kan tafiyar da bamu da wani zabi illa mu bi.

    Tafiya Zuwa ga Wayewa.

    Matakin Wayewa Na Uku– Wayewa

    Wayewa yana faruwa ne lokacin da muka Karɓa daga ƙarshe

    Duk abin da muka koya kuma muka yarda gaskiya ne, bai kasance gaskiya ba.

    Duk da Jinsimmu, Dukiya, Aiki, Mallakar abubuwa,

    Ko kuma wani kwatancen da aka koya mana ya bambanta mu da juna.

    Yanzu mun gane cewa ba mu fi kowa ko kasancewa mafi muhimmanci ba akan wasu ba.

    Za mu fara jin Ruhinmu a ciki, muna rungumar saƙonsa

    Ta hanyar Raba Soyayyar mu ba tare da wani sharaɗi ba.

    Ko da yake abin da muka koya lokacin da muke kanana zai kasance tare da mu (Izza)

    Tasirinsa a rayuwarmu yanzu kaɗan ne.

    Maimakon yin gasa, yanzu muna fatan mu haɗa kai.

    Maimakon mu rayu cikin tsoro, yanzu muna neman mu yi rayuwarmu da soyeyya.

    Kuma maimakon mu yi so abin da yake mafi kyau ga kanmu kaɗai,

    Yanzu muna fatan taimakawa Wasu ba tare da son kai ba, don sauƙaƙe Tafiyarsu ta cikin Rayuwa.

    Da wannan canji da da kuma amincewa da saƙon Ruhi

    Za mu ci gaba da tafiya zuwa ga Wayewa.

    Tare da Farkawa Komai yake Canzawa

    Duk sashin tafiyar.

    Da zarar kun farka, tabbashin da akwai a rayuwarku

    Ba zai taɓa kasancewa ɗaya ba kuma babu ja da baya.

    Duk abin da ke cikin rayuwar ku zai canza, ciki har da abokantaka, dangantaka

    Da kuma haƙuri ga wasannin da mutane ke yi waɗanda suka rage cikin barci.

    Farkawa yana faruwa ne lokacin da

    kuka fara tambayar duk abin da kuka koya.

    Wayewa ko da yake zai faru ne kawai lokacin da kuka

    yarda da duk abinda kuka koya a rayuwa Ba gaskiya bane.

    Gaskiya ako yaushe ta kasance a ciki.

    Tsaurara a nitse ga duk amsoshin da kule nema.

    Wasan

    A ranar da za mu mutu lokacin da Izza ya miƙa wuya

    Shi ya juya rayuwarmu, za mu fahimci rayuwarmu gaba ɗaya wasa ce.

    Duk yin imani ne.

    Mun yi aikin mu da kyau ba mu taɓa sanin ba gaskiya ba ne.

    Rayuwa kawai ruɗi ne, inda dukkanmu ke da sassan mu a cikin wasan.

    Idan muka bi rubutun, kamar yadda muka koyi yi yayin da muke girma,

    Amsoshin da muke nema game da rayuwa za su iya kuɓuce mana.

    Sai kawai lokacin da muka yi aiki a waje da iyakokin rubutun kuma muka farka,

    Amsoshin da muke name za su iya bayyanar da kansu daga karshe.

    Duniyar Ruɗu

    Ruɗu shine duniyar da mafi yawanci suna barci,

    Rayuwa cikin Gaskiyar da Koyar wanda aka Karɓa a Matsayin Gaskiya.

    Waɗanda suka cigaba da kasancewa cikin barci a tsawon rayuwarsu

    suna neman gaskiyarsu a cikin Duniya, suna imanin abin da aka koya musu

    Yayin da suke girma zai kawo musu Ma'ana da Farin Ciki.

    Bazai yi ba.

    Lokacin da muka fara farkawa za mu fara tambayar ko wannan imani daidai ne.

    Duk da yadda rayuwarmu ta kasance da nasara, sauraran muryar da muka fara ji a ciki,

    Ka'idojin da ba kokwanto muka koya kuma muka yarda da su a matsayin gaskiya

    Basu da ma'ana a gare mu kuma.

    Muryar da muke ji tana gaya mana Ƙauna marar Sharaɗi,

    Fata, Daidaito, Taimakawa Wasu, da duk sauran kyawawan ɗabi'u na kulawa

    Rabawa ba tare da son kai ba da duk wasu.

    Duniyar ruɗu da muka taɓa fahimta kuma muka karɓa a matsayin gaskiyar mu

    Ta fara narkewa, tana barin duniyar da ba za a iya ganewa ba,

    Duniyar da So (Ruhi) ya zama rinjaye akan Tsoro (Izza).

    Maimakon a yi fafatawa da juna don tsira a duniya.

    Muna nufin mu taimaki juna a maimakon haka.

    Rayuwa a cikin irin wannan duniyar yana yiwuwa.

    Enjoying the preview?
    Page 1 of 1