Mafarkin Farin Ciki: ZAƁAR SOYEYYA A KAN TSORO
By Ken Luball
()
About this ebook
Reviews for Mafarkin Farin Ciki
0 ratings0 reviews
Book preview
Mafarkin Farin Ciki - Ken Luball
Table of Contents
Mafarkin | Farin ciki:
Abubuwan dake ciki
Gabatarwa: Zuwa ga Yaran Duniya
Babi na 1: Gano Haskenka
Babi na 2: Gabatarwa ga Alakar Hankali, Jiki, da Ruhi
Babi na 3: Bango, Abin rufe fuska, da Kofa
Babi na 4: Gamuwar Hankali, Jiki, Ruhi
Babi na Biyar: Ruhi ke bada Ma’na ga Rayuwarmu
Babi na 6: Ruhi da Wayewa
Babi na 7: Rayuwa cikin Wayewa
Babi na 8: Zaɓar Soyeyya Akan Tsoro
Chapter 9: Rayuwa tare da Ruhi cikin Rayuwarka
Chapter 10: Mafarkin Farinciki
Babi na 11: Ma’anar Rayuwa
Karshe
Waɗanda suke neman farin ciki ta wajen duniya wasu,
Game da Ken
Mafarkin
Farin ciki:
––––––––
ZAƁAR SOYEYYA A KAN TSORO
––––––––
Littafin Ruhaniya Daga Ken Luball
Da Bodhi (Jagoran Ruhi
)
Translator: Nuhu Muhammed Ahmed
Copyright Claimant: Ken Luball
Bayanin Marubuci:
Menene Ma’anar Rayuwa?
Ma’ana na Rayuwa,
Dalilin da muke a raye,
Shine mu saurara a nitse zuwa ga ruhi dake ciki da
Bin kan hanyar da yayi jagora a gare mu.
Akwai Littattafai huɗu a ciki Jerin Littattafai Huɗu Na Farkawar
:
Yau Zan Mutu: Zaɓi a Rayuwa
Shiriyar Ruhi: Tafiya ta Rayuwa
Natsuwarsa: Kauye Na Fata
Mafarkin Farin ciki: Zaɓar Soyeyya a kan Tsoro
Ruhaniya shine imanin akwai yanki na Ubangiji (Ruhi ko Rai) cikin kowane rayuwa kuma, saboda haka kowane rayuwa yana da mahimmanci, Daidaito, da alaka.
Burina na rubuta waɗannan littattafai ya kasance kokarin farkarwa da taimakawa wasu, waɗanda sun kasance a farke, kara cikakken fahimta menene Wayewa, Saboda tafiyar su ta rayuwa ta kara kasancewa cikin cikakken ganewa.
Uku daga cikin waɗannan labarai an rubuta su a mutum na farko, biye da Tafiyar Ruhaniya
ta rayuwar Yaro, yayin da suke koyon darasin da ake bukata domin amsa tambayar da ke sama a cikin fahimta, ban sha"awa, musamman, wanda ba kawai zai ja hankali ba, Amma harda shiga ma.
Bodhi shine Jagoran Ruhina
; ya iya sanad da ni cikin sauki yayin da na rubuta tunaninsa. Duk da tafiyata zuwa Wayewa bai cika ba tukunna, Bodhi, kasancewa mai jagoran Ruhi, mafi hakika ne ya Waye. Mun rubuta wannan littafin ga duka waɗanda suke neman fara bin tsarin farkarwa ko an farka ana nema shiga da nitsa cikin hanyar zuwa ga wayewa.
A tare da soyeyya da goyon bayan Bodhi ne kawai
muka iya rubuta waɗannan littattafai a tare.
Samu karin bayani dangane da kowane ɗaya daga waɗannan littattafai huɗu na Ruhaniya cikin wannan jerin littattafai huɗu a shafin yanar gizo na: http://kenluball.com
Sadaukarwa Zuwa Ga Yaran Duniya
Muna sadaukar da wannan littafin zuwa ga Yaran Duniya. Fatan mu ne iyayen ku, da waɗanda suke son ku, za su karanta wannan littafi, ta hanyar yin haka, su zama masu iya taimaka muku ku zaɓi hanyar ku ta rayuwa cikin hikima. Fatan mu ne tafiyar ku ta kasance cike da soyeyya, farin ciki, da mamaki.
Gabatarwa:
Zuwa ga Yaran Duniya
Text Description automatically generatedYayin da kake girma, za ka gane rayuwa zai bayyana da kalubale sosai.
Duniya bai kasance waje mai daɗin zama ba a ko da yaushe.
Za ka ga abubuwa dayawa wanɗanda zasu sa ka mamakin
Me yasa munanan abubuwa suke faruwa ga wasu da yawa.
Za ka ga mutane waɗanda basu da wadataccen abincin da zasu ci
Ko waje da zasu yi rayuwa, da makamantansu,
Waɗanda basu son wani saboda suna da banbanci.
Saɓanin hoton dake sama, ba tare da la’akari da launin fatar ka,
Kasar da kake rayuwa a ciki, sunanka, addininka,
Kowane sauran bambance-bambance da akwai,
Ya kasance da muhimmanci kar ka yarda wani yafi
Ko fiye da mahimmanci akan wani ba.
Kowane Rai na da Muhimmanci daidai
,
Ba tare fa la’alari da kowane sanannen bambance-bambance dake akwai a tsakanin mu ba.
Yin rayuwa mai kyau bai da alaka da aikin da kake da shi,
Adadin kudin da ka Mallaka,
In kai shaharerre ne ko wani abu na daban da zaka iya ji dangane da
Lokacin da kake girma.
Maimakon haka, abu mafi muhimmanci kawai shine ka kasance mutum na kwarai
.
Ka zama wanda ke kula da yanayin wasu,
Taimakon su duk lokacin da zaka iya,
Kula da kowa da alheri da soyeyya,
Ko da sun kasance basu baka irin wannan kulawar ba.
Zaka ga cewa akwai da yawa a wannan duniya waɗanda basa farin ciki,
A tsorace da kuma damuwa dangane da kansu kawai.
Don Allah, kada
ka zama kamar su.
Zaka iya canja duniya in ka saurara
cikin sauki
Zuwa ga sanyanyar muryar dake cikin zuciyar ka da
Da raba wannan sakon tare da kowa.
Rungumi rayuwa tare da ban mamaki. Kasance mai kyautatawa ga kowa.
Raba kyawawa da suke cikin zuciyar ka tare da Waɗanda suka bambanta ko suke fama.
Da kuma, mafi mahimmanci, kula da wasu
Kamar yanda kake so a kula da kai.
In kayi haka, zaka yi farin ciki.
Kada ka zaɓi yin rayuwa a cikin duniya inda kowa a tsorace yake,
Masu son kai.
Maimakon haka, kula da wasu, kasance mai kyauta, mai tausayi, mai so, mai mutuntawa, mai tawali’u, mai hakuri, mai gaskiya, mai tausayi, mai alheri, tabbatacce, mai godiya, mai fata, da kuma kyakkyawan fata game da rayuwa.
Kasance mai karfin hali; kula game da yanayin wasu,
Kasance mai fara’a da kuma taimakonsu ko sun kasance daban ko cikin bukata.
In kayi haka, zaka iya samun rayuwanka cikin farin ciki da kuma ma"ana.
Hanyar da ka zaɓa ta rayuwa ita ce zata yanke
Makomar duniya.
Mutanen da basu yin aiki mai kyau sosai
Wajen kula da duniyar mu da kuma wasu.
Ya rage naka, saboda haka, domin samad da sauyi
Wannan dole ne a yi,
Ta zaɓar hanyar da ta fi dacewa cikin rayuwa.
"Hangen nesanka zai zama bayyananne
Kawai in zaka iya kallon
Cikin zuciyarka.
Wanda ya kalli waje, zai yi mafarki.
Wanda ya dubi ciki, zai farka".
Carl Jung
Babi na 1:
Gano Haskenka
Amsoshin da muka nema, domin Gano Haskenka
,
Ya bamu damar rungumar kwanciyar hankali, Soyeyya da kuma Ma"ana a cikin rayuwar mu,
Ba zai samu ba a cikin duniya ta hanyar kallon waje.
Zai iya samuwa ne kawai ta hanyar kallon ciki
, idan Ruhi yake.
Yawancin mu cikin fahimta mun gane wannan.
Domin aminta da kuma yarda Ruhi ya jagoranci
Tafiyarka ta rayuwa, duk da haka, da matukar kalubale.
Wannan saboda rinjayen Izza (kai).
Shi Izza ya haɗa da komai da aka Koya mana
da kuma Imanin
kasancewar hakan gaskiya tun haihuwar mu.
Farkawa
yana farawa ne lokacin da muka fara tamabaya dangane da komai da muka Koya
.
Wayewa
na faruwa lokacin da muka Aminta
gaskiya ne
Komai da muka koya ya kasance Ba daidai ba
.
Tafiyar na da tsawo,wahala, da kuma sau da yawa kaɗaici.
Ma"anar rayuwa shine bin wannan tafiya,
Rabawa ba tare da son kai ba
Tare da dukan wasu Haskenka
dake ciki.
"Me yasa muke raye"? Menene "Ma"anar rayuwa? Waɗannan tambayoyi an sha tambayarsu na sawon shekaru dubu; Yana iya zama abin mamaki yadda amsoshin suka kasance asali. Lokacin da aka haifemu, waɗannan amsoshin sun kasance a tare da mu. A gaskiya, ya kasance sai
bayan" an haifemu ne amsoshin ga wanɗannan tambayoyi suka bace a ciki kalubale masu yawa wanda dukanmu muka fuskanta a cikin rayuwa.
"Shekaru biyar na farko na yaron sune mafi mahimmaci". A wannan lokacin ne suke sanin me ake sammani daga garesu yanda zasu ji da yanayi daban-daban cikin duniya. Hakazalika a wannan lokaci zasu bunkasa ra’ayin duniya gabaɗaya da yadda zasu bi da wasu. Ra’ayinsu, mabanbancin ra’ayi, Amanna, da buri sau da yawa suna samuwa ne lokacin waɗannan shekarun farko kuma zai samad da tushen yadda zasu aikata da bi da wasu na tsawon abinda ya saura a rayuwarsu.
Lokacin waɗannan shekarun, idan an koya wa yaro ya ga duniya da wasu ta yanayi marar kyau, daya inda "Tsoro" ya mamaye "Soyeyya", sannan kalubale da suka fuskanta zai zama babba. Ganin duniya ta wannan hanyar, zasu zama masu damuwa da kansu kawai, maimakon ga kowa. Ta rungumar wannan yanayi, Tafiyarsu cikin rayuwa sau da yawa zai kasance cikin kadaici sannan gwagwarmayansu zata yawaita.
Duk da haka, idan, lokacin waɗannan shekarun na farko, sun rungumi "Soyeyya a kan Tsoro", sai rayuwarsu ta dauki mabambancin alkibla sosai. Ta rungumar mahimmancin soyeyya na farko, zasu fara fahimtar rayuwa ta hange na daban; ɗaya idan akwai damuwa da tausayi ga "Kowa", maimakon wa kansu kawai. Waɗannan yara zasu san yadda zasu fahimta da kuma bi da wasu tare da mutuntawa da ganin rayuwa tare da ban mamaki da soyeyya, maimakon tare da tsoro da kiyeyya.
Abinda ake koya lokacin shekaru biyar na farko a rayuwar yaro, zai iya yin tasiri a gabaɗayan rayuwarsu.
Gwagwarmaya da yawa da muka fuskanta tsawon rayuwa sau da yawa sakamakon imani damuka ginu akai lokacin waɗannan shekarun na farko. Mun koyi dangantakar mu game da duniya lokacin waɗannan shekarun sannan za mu iya bata sauran rayuwar mu wurin kokarin gyara barnar da aka aikata. Barnar da aminta da karyar Izza ta haifar, sakonnin da muka karɓa a matsayin gaskiya, yayin da muka fahimci rawar mu a duniya. Lokacin da yaro ya kai fara makaranta, waɗannan sakonni sau da ya sun riga sun dasu a zuciyar yaro, sun yi tasiri ga dukkan tunani da aikin su, sau da yawa ga tunatarwa ta rayuwarsu.
Ina son kayi tunanin buɗaɗɗen akwati. Kafin a haife mu, akwatin fanko ne. Da haifar mu, ko da yake, "kai" (ko Izza), wanda shine komai da muka "koya, da
imanin hakan gaskiya ne",bayan an haife mu, wannan akwati ya fara cika. Da duk wani hulɗa da muka yi, akwatin yake kara nauyi, a yayin da ya fara cika da hayaniyan abubuwan da muke tarawa a ciki, na daga dukkan kura-kuren abubuwa da muka koya lokacin rayuwar mu. Da kara nauyin akwatin, hasken mu yake kara raguwa sannan kuma da yawan abinda zamu cire daga ciki lokacin da muka Farka muka fara tafiyar mu zuwa ga wayewa.
Ɗauke a cikin akwatin akwai dukkan gaskiyar Izza na karya Wanda yaro ya koya da kuma aminta da abinda ya koya yanyin da yake girma. Ko da yake akwatin yakan ɗau tsawon lokaci sosai kafin ya cika, zai iya ɗaukan sauran rayuwarsu, idan ma ya kasance, domin "Gano Haskensu" kuma, fitad da komai daga cikin akwatin da maido da kwanciyar hankali da fahimta wanda suka a sani a baya kafin ya fara cika; kafin a bayyanar da su ga karairayi masu yawa